Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi tir da sabbin hare haren Amurka kan wasu sassan kasar na bakin teku.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Harkokin Wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai wa Iran a cikin awanni 24 da suka gabata, inda ta bayyana wadannan ayyuka a matsayin keta Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, da duk tanade danaden yarjejeniyar tsagaita wuta.
Sanarwar ta jaddada cewa wadannan hare-haren ba wai kawai sun zama karya ka’idojin asali na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ba, a’a har ma sun kasance babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya, wanda hakan ya sa kokarin da aka yi a cikin ‘yan watannin nan na rage tashin hankali da dawo da kwanciyar hankali a Yammacin Asiya ya rushe.
Sanarwar ta kara da cewa ta hanyar kai hari kan kayayyakin more rayuwa na sufuri na Iran, jiragen kamun kifi, jiragen ruwa na dakon kaya, da gine-gine, ta aikata manyan laifukan yaki.”
Ma’aikatar Harkokin Waje ta kara da cewa gwamnatin Amurka, ta hanyar tsoma baki a fili kan aiwatar da shirye-shiryen da suka wajaba a mashigin Hormuz na Iran, ta sake haifar da rashin tsaro a yankin tare da kawo cikas ga jigilar kayayyaki na kasuwanci na kasa da kasa.
Sanarwar ta jaddada kudurin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na kare ikonta da kuma mutuncin yankinta daga farmakin soji na Amurka da na kowane bangare.
Ma’aikatar ta tunatar da kasashen da ke makwabtaka da ita cewa, a karkashin dokokin kasa da kasa, suna da alhakin hana masu kai hari amfani da yankinsu da albarkatunsu don kai hare-haren soji kan Iran, tare da gargadin cewa duk yankin da akayi amfani da shi zai fuskanci martanin Iran.