Kasashen Iran da Oman sun tattauna kan tsara yadda a nan gaba zasu kula da zirgar-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana cewa, kasashen biyu sun yi shawarwari kan daidaita tsare-tsare a nan gaba na kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin, tare da mayar da hankali kan tsaron jiragen ruwa, da ‘yancin cin gashin kan kasashen biyu, da aiwatar da yarjejeniyar Islamabad.
Mista Baqa’i na karin haske ne kan ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya kai Oman, yana mai cewa tattaunawar da aka yi a birnin Muscat na da nufin daidaitawa tsakanin kasashen biyu na mashigin ruwa na Hormuz kan shirye-shiryen da za a yi a nan gaba na gudanar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci.
Ya ce, ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun gana ne domin tattaunawa kan yadda ake tafiyar da zirga-zirgar da jigilar kayayyaki a mashigin Hormuz.
A cewar kakakin, bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayi kan tabbatar da tsaro da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin ruwan Hormuz tare da mutunta ‘yancin mallakar kasashen biyu na gabar tekun, da dokokin da suka dace na kasa da kasa, da kuma bisa tanadi na yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad.
Iran ta jaddada cewa, dole ne a samar da shirye-shirye nan gaba na kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz ta hanyar tuntubar juna tsakanin kasashen biyu, tare da yin la’akari da abubuwan da suka faru a watannin baya-bayan nan, musamman yakin da gwamnatin Amurka da ‘yan sahyoniya suka shelanta kan Iran, in ji shi.
Baqaei ya kara da cewa, Iran da Oman sun amince da ci gaba da tattaunawa a matakai na siyasa da fasaha da doka domin cimma matsaya guda kan tabbatar da tsaron jiragen ruwa a mashigin Hormuz.
Ya kuma bayyana cewa, wata tawaga daga gwamnatin Qatar ta halarci wani bangare na tattaunawar, inda ya bayyana Qatar a matsayin daya daga cikin kasashen yankin da su ma suka taka rawar shiga tsakani a shawarwarin da Amurka da Iran suka yi a baya-bayan nan.