Mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya ce: Tuntubar juna tsakanin Iran da Iraki ya zama wajibi don inganta matakan tsaro tsakanin kasashen biyu
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin siyasa Majid Takht Rawanji ya jaddada da cewa: Ziyarar da ya kai zuwa Iraki ta zo ne bisa tsarin tuntubar juna ta fuskar siyasa da aka saba yi tsakanin kasashen biyu.
Rawanji ya kara da cewa: Iran da Iraki sun tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro tsakaninsu a matsayinsu na kasashen ‘yan’uwa da musulmi, tare da jaddada muhimmancin hadin kai da hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Ya kara da cewa, tsaron yankin shi ne babban fifiko ga kasashen Iran da Iraki, wanda ya bukaci ci gaba da tuntubar juna da kuma yin aiki tare a matakai daban daban na kasashen biyu.