Mai ba da Shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci da tsohon fira ministan Iraki sun jadadda goyon bayansu ga kugiyoyin gwagwarmaya
Mai ba da shawara kan harkokin kasa da kasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tattauna kan ci gaban yankin Gabas ta Tsakiya a wata tattaunawa ta wayar tarho da tsohon fira ministan kasar Iraki Nuri al-Maliki, kuma dukkansu sun jaddada goyon bayansu ga kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa.
A tattaunawar ta wayar tarho, Ali Akbar Welayati, mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasa, ya yi tambaya game da lafiyar tsohon Fira ministan Iraki Nouri al-Maliki.
A cikin kiran, Velayati ya yi fatan samun koshin lafiya ga al-Maliki da samun sauki cikin gaggawa, inda ya yaba da rawar da ya take takawa wajen tallafawa kungiyoyin gwagwarmaya.
Nuri al-Maliki ya kuma nuna jin dadinsa ga yadda Ali Akbar Welayati ya bi diddigin lafiyarsa, yana mai jaddada mahimmancin sadarwa da daidaitawa tsakanin shugabannin kungiyoyin gwagwarmaya.