Iran : Ayyukan Amurka Da Isra’ila Babbar Barazana Ne Ga Duniya

Jakadan Iran kuma Mataimakin Wakilin Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Gholamhossein Darzi, ya bayyana cewa haramtattun ayyukan Amurka da gwamnatin Isra’ila sun zama babbar barazana

Gholamhossein Darzi, Jakadan Iran kuma Mataimakin Wakilin Dindindin a MDD

Jakadan Iran kuma Mataimakin Wakilin Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Gholamhossein Darzi, ya bayyana cewa haramtattun ayyukan Amurka da gwamnatin Isra’ila sun zama babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali, da tsaro na yanki da na duniya baki daya.

Mista Darzi, ya bayyana a taron Kwamitin Tsaro kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.

Ya bayanna cewa “Duk da sanarwar tsagaita wuta, Gaza na ci gaba da zama cikin rudani da kuma killacewa.

Gwamnatin mamayar Isra’ila ta ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar hare-haren soji da kuma tsauraran matakai kan hanyoyin samar da agajin jin kai.” “

“A lokaci guda, jami’in diflomatsiyar na Iran ya bayyana cewa gwamnatin Isra’ila ta ci gaba da fadada matsugunan da ta ke yi ba bisa ka’ida ba a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, wanda hakan ya zama babban keta dokokin kasa da kasa da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da aka aminta da su.”

Mataimakin Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ce: “Ayyukan ta’addanci da Isra’ila ke yi wa Lebanon da kuma ci gaba da keta hurumin Siriya suna kara barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin, wanda barazana ne ga zaman lafiya da tsaro na duniya.”

Mista Darzi ya jaddada cewa: “A cikin wannan mahallin, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake nanata cewa duk wata mafita dole ne ta tabbatar da tsagaita wuta na dindindin, samun damar kai agajin jin kai ba tare da wani cikas ba, da janye sojojin mamaye na Isra’ila gaba daya, da kuma cikakiyar memba ga Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted