Iraki: ‘Yan gwagwarmaya sun kai farmaki kan sojojin Isra’ila a yankunan Falastinu da suka mamaye

Dakarun Islama a Iraki sun ce sun kai wani sabon farmaki kan wasu sansanonin sojin Isra’ila a cikin yankunan Falasdinawa da suka mamaye. Kungiyar gamayyar

Dakarun Islama a Iraki sun ce sun kai wani sabon farmaki kan wasu sansanonin sojin Isra’ila a cikin yankunan Falasdinawa da suka mamaye.

Kungiyar gamayyar kungiyoyin gwagwarmayar Iraki ta ce jiragenta marasa matuka a safiyar wannan  Litinin sun kai wani muhimmin hari a Umm Al-Rashrash da aka fi sani da Eilat a kudancin Falastinu da yahudawa suka mamaye.

“A ci gaba da tunkarar mamayar da muke yi, da kuma goyon bayan al’ummarmu a Palastinu da Lebanon, da kuma mayar da martani ga kisan kiyashin da ‘yan ta’addan sahyuniya suke yi wa fararen hula da suka hada da yara, mata da tsofaffi, mayakan gwagwarmaya a Iraki sun kai hari kan wata muhimmiyar cibiya a  (“Eilat”) ” in ji ‘yan gwagwarmaya.

Sabon harin ya zo ne kwana guda bayan da kungiyar ta sanar da kai hari kan wasu wurare uku na Isra’ila a yanki guda.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ta nanata cewa hare-haren da ake kai wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na goyon bayan Palasdinawa da al’ummar Lebanon da ake zalunta ne.

A cikin watannin da suka gabata, kungiyar gwagwarmaya ta kuma kai hari kan sansanonin sojojin Amurka da dama a Iraki da Siriya saboda goyon bayan Washington ga gwamnatin Isra’ila da laifukan ta.

Tun a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ne kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Iraki ta fara gudanar da irin wadannan hare-hare kan wasu muhimman wurare da ke cikin falastinu da ke karkashin mamayar yahudawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments