Jakadan kasar Irak a washintong ya bayyana cewa kasar Iraki entacciyar kasa she, tana da yencin kulla yarjeniyar tsaro da ko wace kasa da take so, wannan bayan korafin da gwamnatin Amurka tayi na yarjeniyar tsaro wacce kasar Iraki ta kulla da JMI.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jakadan yana cewa, kasar Iraki tana da yencin kulla yarjeniyar tsaro da kasashe makobta musamman kasar Iran wacce take da iyaka da mai tsawo da ita don samun amincin a kan iyakokin kasashen biyu. Ba ruwammu da abinda wani yake yake cewa.
Tehran ta bagdaza dai suna da dangantakan tsaro mai karfi da juna, tun bayan samun nasara da Daesh, kuma suna haka kai don tabbatar da cewa an ci gaba da samun zaman lafiya a kan iyakokin kasashen biyu.
Ya ce korafin da gwamnatin Amurka ta yi kan wannan yarjeniyar, ci gaba ne na shishigin da gwamnatin Amurka take yi a cikin al-amuran harkokin cikin gida na kasar ta Iraki.
Amma kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka Tammy Bruce ya bayyana rashin amincewar Amurka da yarjeniyar amma bai bayyana wani abu ba. A ranar litinin ce Dr Ali Larijani babban sakataren majalisar koli ta harkokin tsaron kasar Iran ya rattaba hannu kan yarjeniyar a madadin Iran sannan tokwaransa na kasar Iraki Araji ya sanya hannu a madadin Iraki.
Larijani ya isa bernin Beirut na kasar Lebanon inda ya sami kekyawar tarba kafin ya gana da shugaban kasa Josept Aun da kuma shugaban majalisar dokokin kasar.