Firai ministan kasar Iraki Mohammad Shia Assudani ya bayyana cewa gwamnatinsa bata tushe asusun kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon da kuma Ansarallah ta kasar Yemewn ba.
Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran IP ya nakalto sudanina cewa gwamnatinsa tana kokarin hana tasowar wani riki a yankin sannan da kuma kaucewa duk wani rikicin siyasa a cikin gida ne, tare da wasu matakan da ta dauka.
Yace babu wani shiri na daukar Hizbullah da Ansarullah a matsayin kungiyoyin yan ta’adda. Y ace kasar Iraki bata adawa da wadan nan kungiyoyi sannan basa da kadarori a kasar wadanda za’a kwace ko a hanasu amfani da su.
Y ace matsayin Iraki a kan wadan nan kungiyoyi da kuma palasdinu baya canzawa. Kungiyar ISIS ce aka haramta kuma har yanzun dokokin haramtata suna nan.
\