Iraki Na Samun Zaman Lafiya Kuma Tana Kokarin Kawo Karshen Zaman Sojojin Ketare A Kasar

Prime ministan kasar Iraki shiya Al-sudani ya sanar a birnin bagadaza cewa sun fara shirin kula wata yarjejeniya a hukumace da kasar Amurka, da zai

Prime ministan kasar Iraki shiya Al-sudani ya sanar a birnin bagadaza cewa sun fara shirin kula wata yarjejeniya a hukumace da kasar Amurka, da zai kai ga ficewar sojojin kasashen waje daka kasar, daga nan zuwa wata satumbar shekara ta 2026, wanda wannan wata ishara ce ta bude wani sabon shafi a kasar na zaman tabbaci da tsaro mai dorewa.

Kasar iraki na kokari wajen ganin an kawo karshen zaman sojojin mamayar Amurka dake kasar fiye da shekaru 20 da kuma tsoma bakin kasashen wajen, da ya fara daga lokacin da Washington ta shiga kasar a shekara ta 2003 domin kaddamar da hare-hare da dukkan duniya ta yi tir da shi da kuma bayyana shi a matsayin wanda ya sabama doka.

A wata hira da aka yi da prime ministan iraki a yau Asabar Al sudani ya tabbatar da cewa iraki ta fara tattaunawa kai tsaye da Amurka dake jagorantar mamayar Iraki tun lokacin kirkiro kungiyar Daesh a shekara ta 2014 , yace yanayin tsaro da ake ciki a kasar baya bukatar ci gaba da zaman sojojin mamaya baki daya.

Washington da Bagadaza sun cimma yarjejeniyar fara ficewar sojojin Amurka daga Iraki a shekara ta 2024 musamman daga muhimman sansaninsu kamar Ainul asad dake yammcin kasar, da kuma sansanin Camp Victoriya dake kusa da bagadaza, kuma an tsara zaa kammala janyewar a satumbar shekara ta 2025.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments