Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Iraki ta sanar a ranar Lahadi cewa adadin masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen da aka gudanar ya kai kashi 82.42%, wanda ya tabbatar da sahihanci da kyakkyawan tsarin gudanar zaɓen, a cewar hukumar.
Shugaban Hukumar Omar Ahmed, ya bayyana a yayin wani taron manema labarai cewa hukumar ta nuna daidaito da adalaci ga dukkan ‘yan Takara.
Ahmed ya bayyana cewa hukumar ta sa ido kan tsarin zaɓe a duk faɗin jihohin ƙasar ta hanyar ƙungiyoyin da ke aiki, yana mai jaddada cewa sakamakon ya nuna jajircewar masu kaɗa ƙuri’a da kuma tafiyar da harkokin zaɓe cikin sauƙi da kuma sahihin tsari.
A cikin wannan yanayi, mai ba da shawara kan harkokin shari’a na hukumar Hassan Salman, ya tabbatar da cewa tsarin zaɓen ya yi armashi kuma an gudanar da shi ba tare da wani cikas ko keta doka ba, yana mai nuna cewa fitowar jama’a a zaben ya zama abin buga misali, domin kuwa ba a taɓa yin irinsa ba.
Salman ya ƙara da cewa na’urori suna aiki da inganci sosai a duk lokacin zaɓen, kuma ba a sami wata matsala ta fasaha ko katsewar layukan yanar gizo ba, yana mai jaddada cewa hukumar ta ci gaba da ayyukanta don tabbatar da gaskiya da sahihancin tsarin zaɓen.
An fara gudanar da zaɓen ‘yan majalisar dokoki na musamman na shekarar 2025 a safiyar jiya Lahadi, a tsakiyar tsauraran matakan tsaro da kuma tsarin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (IHEC) ta tsara domin tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.
Wannan zabe na musamman ne da aka gudanar kafin zabe na gama gari a ranar 11 ga watan Nuwamba.