HKI Ta Jefa Boma-Bomai A Kan Asbiti Tilo Da Ya Rage Yake Aiki A Arewacin Gaza

Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau

Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau Lahadi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun wargaza bangaren ’emagencu’ bukatar kula na gaggawa a asbitin da kuma kofar shiga asbitin. Har’ila yau hare-haren sun lalata bangaren Iskar Oxigen na kula da wadanda suke bukatar kula mai tsanani a asbiti. Kuma sanadiyyar haka mutane da dama sun rasa rayukansu awannan bangaren daga ciki har da wani yaro dan shekara 12 wanda ya ji rauni a kai.

Razan Al-Nahhas wani likita mai aiki a bangaren  kula na gaggawa a asbitin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa wannan asbitin ne kawai dama yake aiki a arewacin Gaza, kuma a halin yanzu babu wani asbitin da ya rage a yankin.

Labarin ya kara da cewa bayan  wadannan hare-hare kan asbitin na Al-Ahli, mutane da dama basu san inda zasu je don samun jinya ba.

Likitan ta kara da cewa kafin hare-hare na safiyar yau Lahadi dai marasa lafiya wadanda aka yankewa kafafu da kuma wadanda suka ji rauni a kai da kuma kirjinsu ne suka fi yawa a cikinsa. Sannan a halin yanzu babu inda zasu je sai wasu kananan asbitoci wadanda basu da kayakin aiki na kula da su. Kuma tuni wasu sun mutu bayan harin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments