Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Keta Hurumin Masallacin Kudus Da ‘Yan Sahayoniya Su Ka Yi

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da bayani da ya kunshi yin Allawadai da keta hurumin masallacin kudus da ‘yan sahayoniya su ka yi

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da bayani da ya kunshi yin Allawadai da keta hurumin masallacin kudus da ‘yan sahayoniya su ka yi a cikin kwanaki uku a jere.

“Yan sahayoniyar dai sun rika shiga cikin  harabar masallacin na Kudus, suna yin ibadunsu na yahudanci, tare da kariyar ‘yan sandan HKI.

Kungiyar ta Hizbullah ta kuma ce; Abinda ‘yan sahayoniyar suke yi nuna kiyayya ne, da keta hurumin masallacin kudus.

Bugu da kari sanarwar ta kara da cewa; Abinda ;yan sahayoniyar suke yi, ya  isa bakantawa musulmi al’ummunsu da gwmanatocinsu, ya kuma sa su yunkurawa domin hana ci gaba da abinda yake faruwa.

Hizbullah ta kuma ce; Al’ummarmu ta larabawa da musulmi tana da cikakkiyar masaniya akan bukatar a daga murya da karfi  da kuma yin dukkanin abinda ya kamata domin fuskantar wannan keta hurumin, saboda yin shiru yana kara karfafa abokan gaba akan abinda suke yi a cikin Kudus, yammacin kogin Jordan, Syria da kuma Yemen.

Bayanin na kungiyar Hizbullah ya kuma yi kira ga kungiyoyin kasashen musulmi da na larabawa da kuma cibiyoyin addini da malamai ma ‘yantattu a duk duniya da su yunkura da sauri, su kuma dauki nauyin da ya rataya a wuyansu na tarihi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments