Hizbullah, Ta Kai Hari Akan Babbar Hedikwatar Tsaron Isra’ila

Hizbullah Ta Kai Wa Babbar Shalkwatar Sojan HKI Hari Da Makaman Katiusha A cigaba da taimaka wa mutanen Gaza da ake yi wa kisan kiyashi,

Hizbullah Ta Kai Wa Babbar Shalkwatar Sojan HKI Hari Da Makaman Katiusha

A cigaba da taimaka wa mutanen Gaza da ake yi wa kisan kiyashi, kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta kai wasu jerin hare-hare aka babbar shalkwatar sojan HKi dake Iyilit, ta hanayar amfani da makamai masu linzami samfurin Katiuha.

A wata sanarwa da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a jiya Juma’a, ta bayyana kai hare-haren ne akan cibiyar soja ta “Iyilit” da kuma cibiyar rundunar soja ta 769 ta hanyar harba makamai masu linzami samfurin Katiusha.

Dangane da mayar da martani akan harin da sojojin HKI su ka kai wa garin _Kafar-shuba da Markaba da Khiyam a kudancin Lebanon, dakarun na Hizbullah sun sanar da kai hare-hare akan cibiyar rundunar sojan HKi ta 91 da kuma barikin soja na 796 dake kiriyat Shemona.

 Har ila yau sanarwar kungiyar Hizbullah ta amabci cewa, dakarun nata sun kai wani harin akan sansanin ‘yan share wuri zauna na “Shalomi”,haka nan kuma wani sansanin ‘yan share wuri zauna na Kiriyat shimona,inda makiya su ka yi furuci da cewa ya yi barna.

A can sansanin ‘yan share wuri zauna na “Shalomi’ an ga hayaki yana tashi sanadiyyar hare-hare daga Lebanon.

Kakafen watsa laabrun HKI sun ce a cikin watanni 9 na yaki, Hizbullah ta yi nasarar mayar da Arewacin HKI zama wani yanki na tsaro wanda mazaunansa su ka kaurace masa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments