Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana harin da Amurka ta kai kan jirgin ruwan ta a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma.
Kakakin hedikwatar Khatam al-Anbiya ya yi Allah wadai da wannan aika-aika da rundunar sojin ruwan Amurka ta aikata.
A cewarsa Amurka ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta kuma ta aikata fashin teku ta hanyar harin wani jirgin ruwan ‘yan kasuwa na Iran a cikin ruwan Tekun Oman,” in ji Laftanar-Kanar Ebrahim Zolfaghari.
“Muna gargadin cewa rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani nan ba da jimawa ba kan wannan fashin teku,” in ji shi.
Sojojin Amurka sun kai harin ba tare da wani dalili ba kan jirgin ruwan Iran mai suna Toska, wanda ke tafiya cikin kwanciyar hankali daga China zuwa Iran ta cikin Tekun Oman.
A martanin gaggawa, sojojin Iran sun kai hari kan jiragen ruwan Amurka da dama a yankin da jiragen sama marasa matuki.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alfahari da cewa sojojin Amurka sun kwace jirgin ruwan Iran, yana mai kiran sojojin Amurka da “babbar rundunar soja a duniya,” wanda yanzu aka sake fallasa shi a matsayin babban mai fashin teku a cikin ruwan kasa da kasa.