IRGC : Iran ta cike gibin makamai masu linzami da na jiragai marasa matuka a yayin tsagaita wuta

Bayanai da dakarun kare juyin juya halin Musulinci na iran suka fitar ya nuna cewa kasar ta samu nasarar cike gibin makamai masu linzami da na jiragai marasa matuka a lokacin yarjejeniyar tsagaita wutar makonni biyu da aka cimma. Janar Seyyed Majid Mousavi, kwamandan rundunar sojin sama ta juyin juya halin Musulunci (IRGC), ya yi […]
Iran : Harin Amurka kan jirgin ruwan Iran ya saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana harin da Amurka ta kai kan jirgin ruwan ta a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma. Kakakin hedikwatar Khatam al-Anbiya ya yi Allah wadai da wannan aika-aika da rundunar sojin ruwan Amurka ta aikata. A cewarsa Amurka ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta kuma ta aikata fashin teku […]
Iran : Mutum 3,375 sukayi shahada a cikin kwanaki 40 na yakin

Hukumar binciken laifuka ta Iran ta ce akalla mutane 3,375 ciki har da daruruwan yara, suka yi shahada a cikin kwanaki 40 na yakin da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka kaddamar kan kasar. Abbas Masjedi, shugaban kungiyar likitoci ta Iran, ya fada a ranar Litinin cewa yakin, yakin wanda ya fara a ranar 28 ga […]
Araghchi : Amurka ba da gaske ta ke ba a cikin mu’amalarta da Iran

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa Amurka ba da gaske ta ke yi ba a cikin mu’amalarta da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. M. Araghchi ya yi wannan furuci ne a lokacin ganawa ta wayar tarho da takwaransa na Pakistan, Muhammad Ishaq Dar, a ranar Lahadi, yayin da rahotanni ke cewa Islamabad za […]
Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ga Malaman Ahlus-Sunna Na Lardin Hormozgan

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya nuna godiya da kuma jinjinawarsa ga malaman Ahlus- Sunna saboda girmamawa da biyayyarsu ga jagorancin kasa A cikin wani sako da ya aike wa malaman Ahlus-Sunna a lardin Hormozgan da ke kudancin Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Seyyed Mojtaba Khamenei, ya nuna godiyarsa ga malaman addini da […]
Shugaban Iran: Al’ummar Iran Ba Za Su Mika Wuya Ga Matsin Lamba Ba

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Al’ummar Iran ba za su mika wuya ga matsin lamba ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Amurkawa suna neman Iran ta mika wuya ga munanan manufofinta, yana mai jaddada cewa, mutanen Iran ba za su mika wuya ga duk wani matsin lamba daga masu girman […]
Araqchi Ya Tattauna Da Takwarorinsa Na Rasha Da Pakistan

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tattauna mafi mahimmancin batu da takwarorinsa na Rasha da Pakistan Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov da kuma na Pakistan Mohammad Is’haq Dar game da sabbin abubuwan da suka faru a yankin. A cikin tattaunawarsa da takwaransa […]
Qalibaf Ya Ce: Al’ummar Iran Ba Zasu Amince Da Tattaunawa Karkashin Barazana Ba

Kakakin Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Ba za su taba yarda da tattaunawa ba a ƙarƙashin barazana Kakakin Majalisar Shawarar Musulunci wato Majalisar Dokokin Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Shugaban Amurka Donald Trump yana da niyyar mayar da teburin tattaunawa zuwa teburin mika wuya, yana mai jaddada cewa: “Iran ba […]
Jami’in Iran: Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Alkawarin Da Ya Sabawa Dokokin Duniya

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da duk wani alkawari da ya saba wa dokokin duniya Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Iran Sa’id Khatib-zadeh ya jaddada cewa: Shugaban Majalisar Shawarwari ta Musulunci (wato Majalisar Dokoki) da Ministan Harkokin Waje sun bayyana a taronsu na baya-bayan nan […]