Daya daga cikin fitattun jagororin Falastinawa ‘yan gwagwarmaya Usama Hamdan ya bayyana cewa, Benjamin Netanyahu ba a shirye yake ya amince da duk wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta ba.
Jaridar Isra’ila ta Walla ta bayar da wani rahoto da ke cewa, Isra’ila ta yanke shawarar ci gaba da luguden wuta a yankin Gaza da ta mamaye domin ƙara samun dama a shirin tattaunawa ta tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni, .
“Kwanakin baya majalisar tsaron Isra’ila ta bayar da umarni ga sojoji su ƙara ƙaimi a hare-haren da suke kai wa Gaza da zummar ƙarfafa matsayinsu a wajen tattaunawar da ake yi,” in ji jaridar Walla, wadda ta ambato wasu majiyoyi na siyasa.
Sojojin Isra’ila sun jikkata wata Bafalasɗiniya ‘yar jarida da ke aika rahotanni daga yankin Khan Younis na Gaza da aka mamaye.
Dakarun mamaya na Isra’ila sun yi harbi kai-tsaye kan wata tawagar ‘yan jarida, inda suka samu Salma al-Qadoumi a baya, kamar yadda ganau suka shaida wa Anadolu Agency.