Hamas ta yi tir da “mummunan kisan kiyashin” Isra’ila a Gaza

Kungiyar Hamas ta yi kakkausar suka kan “mummunan kisan kiyashi” da gwamnatin Tel Aviv ta yi wa kananan yara da mata na Palasdinawa, yayin da

Kungiyar Hamas ta yi kakkausar suka kan “mummunan kisan kiyashi” da gwamnatin Tel Aviv ta yi wa kananan yara da mata na Palasdinawa, yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare ta sama a zirin Gaza duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Akalla Falasdinawa bakwai da suka hada da mata biyu ne aka kashe a ranar Asabar a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama, a cewar hukumomin lafiya a zirin Gaza.

Masu aikin ceto sun ce wasu mutane 15 da suka hada da yara kanana sun jikkata lokacin da wani hari ta sama kan wani katafaren sansanin da ke tsakiyar birnin Gaza.

Harin dai ya zo ne a daidai lokacin da aka fara tattaunawa a birnin Alkahira, babban birnin Masar, tsakanin masu shiga tsakani, da kungiyar Hamas da kuma sauran bangarorin Falesdinu, da nufin kiyaye yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

A cikin wata sanarwa da kakakin Hamas Hazem Qassem ya fitar ta kafar Telegram ya ce gwamnatin Tel Aviv ta yi wani mummunan kisan kiyashi kan yara da mata (…) a wani bangare na ci gaba da yakin da take yi kan fararen hula.

Yarjejeniya da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar, wadda ta fara aiki a watan Oktoban shekarar 2025, ba ta haifar da tsagaita bude wuta da Isra’ila ba. Akasin haka ma, ta ba wa gwamnatin mamaya damar cin karenta babu babbaka a yankin.

Tun daga wannan lokacin, akalla mutane 950 ne suka mutu sannan wasu 2,935 suka jikkata a hare-haren da gwamnatin Isra’ila ke kaiwa Gaza, a cewar ma’aikatar lafiya ta yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted