Search
Close this search box.

Hamas Da Jihadul Islami Sun Dauki Alhakin kai Harin Tel Aviv

Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa na Hamas da Islamic Jihad da ke Gaza sun dauki alhakin harin bam da aka kai a birnin Tel Aviv. A cikin

Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa na Hamas da Islamic Jihad da ke Gaza sun dauki alhakin harin bam da aka kai a birnin Tel Aviv.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau, rundunar al-Qassam Brigades, reshen soji na Hamas, ta ce ta gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwar dakarun Saraya al-Quds, reshen soji na kungiyar Jihad Islami a yammacin jiya Lahadi.

Har ila yau, ta yi gargadin cewa za a kara kai hare-hare na daukar fansa a yankunan da Isra’ila ta mamaye, muddin Isra’ila ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na kisan kiyashi da kisan gilla da kuma korar Falasdinawa daga muhallansu.

Kwamandan ‘yan sandan gundumar Ayalon Haim Bublil ya yi wannan ikirarin ne a ranar Litinin din nan dangane da fashewar wani bam wanda wani mutum yake dauke da shi a cikin jaka a bayansa yayin da yake tafiya kan titin Lehi a kudancin Tel Aviv lokacin da bam din ya tashi.

Bublil ya shaida wa gidan rediyon Kan na Isra’ila cewa mai yiwuwa maharin ya yi shirin zuwa majami’ar da ke kusa, ko kuma wata cibiyar kasuwanci. Har yanzu ba za mu iya fahimtar dalilin da ya sa ya aka kai harin a wannan lokacin ba.”

A halin da ake ciki, babban sufetun ‘yan sanda na gundumar Tel Aviv, Sufeto Peretz Amar, ya isa a wurin da lamarin ya faru.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments