Jaridar HKI ta Haarets ta buga labarin dake cewa; Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da tsagaita wutar yakin Lebanon ba tare da ya tuntun Isra’ila ba, da hakan ta tilasta wa Benjamine Netanyahu amincewa.
Jaridar ta ci gaba da cewa, abinda ya farun, ya haifar da cecekuce da sabani a tsakanin ‘yan sahayoniya.
Marubucin wata kasida a jaridar ta Haaretz , Amus Harel ya ce; Abinda ya faru, wani maimaici ne na abinda ya faru a Gaza a shekarar da ta gabata, kuma abu ne mai yiyuwa, Trump ya tilasta wa Isra’ila ficewa daga wuraren da ta mamaye a cikin Lebanon.
Marubucin ya kuma kara da cewa; Sau biyu irin hakan tana faruwa da Netanyahu akan yakin Iran, da Trump ya tilasta masa dakatar da yaki, alhali shi yana son a ci gaba.
Netanyahu yana shan suka a tsakanin ‘yan sahayoniya da suke ganin cewa siyasarsu ta waje tana hannun Amurka ne, ba a hannunsu ba.
Dama dai, masu sharhi da dama suna bayyana cewa, Isra’ila tana a matsayin wani makami ne a hannun Amurka da take amfani da shi a cikin wannan yankin na yammacin Asiya.