Gwamnatin Sudan Ta Amince Da Shawarar Tsagaita Wuta Da ‘Yan Tawayen Kasar

Gwamnatin Sudan ta yi maraba da shawarar tsagaita wuta da Amurka ta gabatar, yayin da wata kotu a kasar ta yanke hukuncin kisa kan Jagoran

Gwamnatin Sudan ta yi maraba da shawarar tsagaita wuta da Amurka ta gabatar, yayin da wata kotu a kasar ta yanke hukuncin kisa kan Jagoran ‘yan tawaye a bayan idonsa

Majalisar Tsaro ta Sudan ta yi maraba da kokarin shiga tsakani don kawo karshen rikicin kasar. Bayan wannan sanarwar, wata kotu a Port Sudan ta yanke hukuncin kisa kan kwamandan Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta Rapid Support Forces Mohamed Hamdan Dagalo da wasu mukarrabansa a bayan idonsu. A halin yanzu, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa yara 825,000 ‘yan kasa da shekaru biyar suna fama da rashin abinci mai gina jiki mai tsanani a Sudan.

Yayin da rikicin Sudan ke ci gaba da tsananta, Majalisar Tsaro ta fitar da wata sanarwa tana maraba da kokarin shiga tsakani don kawo karshen rikicin da kuma tabbatar da Shirin gwamnatin Sudan ga duk wani tsarin da ke kare hadin kan kasar, ‘yancin kai, da kuma ci gaba da kasancewar Sudan kasa daya dunkulalliya. Majalisar ta amince da shawarar Amurka na dakatar da yakin amma ba ta bayyana cikakkun bayanai ba.

Amurka ta gabatar da shawarar tsagaita wuta na kwanaki 90 tsakanin sojojin Sudan da Kungiyar Rapid Support Forces, wanda za a bi shi da shirye-shiryen tsaro a matsayin farkon cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin a Sudan. A cewar jami’an Sudan biyu, gwamnati ta gindaya sharadin janyewar sojojin kungiyar Rapid Support Forces daga dukkan biranen da suka kwace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted