Mataimakin ministan harkokin wajen Kazim Gharib abada ya bayyana cewa mashigar ruwa ta Hurmuz ba zata sake komawa kamar yanda take kafin yaki ba. Kuma duk wani kokari na yin hakan zai gamu da maida martani mai tsanani.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto mataimakin ministan yana fadar haka a wani shirin mai suna “lokacin Iran” a daren jiya Talata. Ya kuma kara da cewa, idan majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta amince Iran tana iya ficewa da ga yarjeniyar NPT amma tare da lura da abinda hakan zai jawowa kasar a bangarori da dama.
Gharib Abada ya kara da cewa a halin yanzu dai hulda da hukumar makamashin nukliya ta IAEA ya ragu sosai, kuma a halin yanzu ba su da wuraren da suke bincike a cikin kasar sai kadan, kuma wurare ne ba wasu muhimmanci suke da shi sosai ba. Kuma sun hada da cibiyar bada wutan lantarki na Bushar da wasu wurare.
Amma hukumar bata da damar shiga kasar don gudanar da bincike a manya manyan wurare kamar Furdo Natan da Esfhan ba.
Ministan ya ce, tattaunawa tsakanin Iran da Omman bata da wani dangantaka da Amurka ko kuma yakin da ke faruwa. Ana magana ne kawai kan yanda kasashen biyu zasu kula da mashigar ruwa ta Hurmuz.
Sannan ko Omman ta yarda ko bada yard aba, tunda mashigar ruwan ta shafi tsaron kasar Iran ba abinda zai canza a matsakin da Iran ta dauka kan mashigar. Iran tana tattaunawa da Omman ne kawai don kada wani yace an nuna mata karfi.