Gaza: Shahidai Fiye Da 40 A Khan Yunus Bayan Hare Hare Ta Sama Wanda Jiragen Yakin HKI Suka Kai

A rana ta 293 da fara yakin Tufanul Aksa, jiragen saman HKI sun kai hare hare kan yankuna daban daban inda falasdinawa da dama suka

A rana ta 293 da fara yakin Tufanul Aksa, jiragen saman HKI sun kai hare hare kan yankuna daban daban inda falasdinawa da dama suka yi shahada a yayinsa wasu suka ji rauni.

Falasdinawa fiye da 40 ne suka yi shahada a zirin Gaza cikin sa’I’ii 24 da suka gabata, sanadiyyar hare haren jiragen yakin HKI da kuma makaman igwa.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta kara da cewa jiragen yakin HKI sun kai hare hare ta sama a kan kauyen Alkarah kusa da Khan Yunus da kuma wani yanki da ake kira Dawwar Bani Suhail inda wasu falasdinawa suka yi shahada.

A wasu hare haren da tankunan yaki a cikin garin Rafah kudancin Gaza, sojojin yahudawan sun yi barin wuta a sansanin yan gudun hijira ta Shaburah dake tsakiyar garin Rafah, har ila yau sun kai irin wadannan hare hare a yankuna arewa da kuma yammacin garin na Rafah, inda suka kashe Falasdinawa da dama.

A sansanin yan gudun hijira na Al-Buraij yahudawan sun raunata falasdinawa akalla 7 mafi yawansu yara kanana.

Yawan Falasdinawa da suka yi shahada a Gaza tun fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban da ya gabata ya kai mutum 39,145 a yayinda wasu 90,257 suka ji rauni mafi yawansu mata da yara

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments