Rahotanni daga yankin Gaza suna cewa a yau Talata Falasdinawa 10 sun yi shahada daga cikinsu da akwai karamin yaro da mace, kamar kuma yadda aka sami wadanda su ka jikkata.
Majiyar asibitocin yankin na Gaza sun tabbatar da shahadar mutane 10 da kuma jikkatar wasu da dama sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI ta kai a sassa mabanbanta da su ka hada da Jabaliya.
Bugu da kari majiyar ta ambaci cewa, sojojin mamayar na HKI sun kai hari akan wurin bincike na ‘yan sanda tare da kashe DPO Muhammad Salim da wasu jami’an ‘yan sandan da dama.
Sansanin ‘yan sandan da sojojin mamayar su ka kai wa harin yana cikin kasuwa ne wacce take makare da masu saye da sayarwa.
Masu bin diddigin abinda yake faurwa a yankin Gazan sun bayyana cewa, manufar kai wannan harin, shi ne rusa ginshikin tsaro a yankin na Gaza.
Tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a Gaza, HKI ba ta taba girmamata ba, saboda yadda a kowace rana take kai wa yankin hare.