Falasdinawa 4 Sun Yi Shahada Sanadiyyar Hare-haren Sojojin Sahayoniya

Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa Falasdinawa 4 sun yi shahada a cikinsu akwai kananan yara 2,yayin da wani adadi mai yaw ana
jana'izarShahidai

Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa Falasdinawa 4 sun yi shahada a cikinsu akwai kananan yara 2,yayin da wani adadi mai yaw ana Falasdinawan ya jikkata.

A jiya laraba ne dai sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai hare-hare a yankuna mabananta na kudanci, tsaiya da arewacin yankin Gaza, sun kuma ci gaba da kai hare-haren har zuwa safiyar yau Alhamis.

A yankin kudancin Gaza, harin na Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya shafi sansanin ‘yan hijira a Mawasi a yammacin Khan-Yunus da shi ne ya yi sanadiyyar shahadar mutane biyu. A tsakanin shahidan da akwai yarinya ‘yar shekaru 8, sai kuma wasu mutane 3 da su ka jikkata,daya daga cikinsu rai kwakwai mutu kwakwai.

Harin  na Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya yi sanadiyyar rusa hemomi masu yawa na ‘yan hijira a yankin da ya mayar da ‘yan hijira masu yawa ba su da matsuguni.

A gundumar “Wust” wani jariri mai shan nono mai suna Muhammad Nofal ne ya yi shahada,sai kuma wasu Falasdinawa masu yawa da su ka yi shahada.

Hare-haren safiyar yau Alhamis kuwa sun shafi hemomin ‘yan hijira wanda kuma ya jikkata Falasdinawa 13 da kananan yara 8,kamar yadda asibitin “al-shifa” ya bayyana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted