IRGC Na Iran Sun Sanar Da Kona Rumbunan Ajiyar Manfetur Na Yarima Hassan Dake Jodan

Dakarun kare juyin musulunci na kasar Iran sun sanar cewa sun samu nasarar kai kai hari kan rumbunan manfetur da wuraren adana harsashai a sansanin

Dakarun kare juyin musulunci na kasar Iran sun sanar cewa sun samu nasarar kai kai hari kan rumbunan manfetur da wuraren adana harsashai a sansanin soji na yarima hassan na jodan , kuma ya kama da wuta a matsayin martani kan harin soji da Amurka ta kaiwa iran

ofishin dake kula da hulda da jama’a na dakarun kare juyin musulunci na iran ta sanar a litinin cewa wannan matakin wani bangare ne martanin da aka mayar kan harin da kasar Amurka ta kai kan sansanonin bakin taku na iran da kayayyakin bukatar rayuwa da na sadarwa a kudancin kasar.

haka zalika dakarun kare juyin musulunci na iran sun yi gargadin cewa duk wani matakin wuce gona da iri da Amurka za ta dauka kan kasar iran zai fuskanci mayar da martani mafi muni da ba tayi tsammani ba.

sojojin iran sun kai hare-hare da jiragen sama mara matuki alokacin guda kuma ta kai akan wasu wurare dake da alaka da kasar Amurka, da ya hada da tsaron sararin samaniya na Patriot da ma’ajiyar harsasai da wurin rada a kasar Kuwait da kuma cibiyoyin sadarwa da rada a kasar Baharain.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted