Rahotannin sun nuna cewa dakarun kare juyi musulunci na iran IRGC ta bayanna cewar dakarunta sun kai harin mayar da martani kan muhimman wuraren soji na Amurka a sansaninta dake Baharain, da ya hada da babbar hedkwatarta ta biyar ,
Haka kuma sun kai hari da makamin mai linzimi kan sansaninta dake kasar Jodan a matsayin mayar da martani kan keta yarjejeniya da Amurka take yi da aka cimma
Yace Amurka na amfani da sansaninta na jodan ne wajen kai ma iran hari, yanzu an tilasta wa Amurka ta biya diyya kan laifukan da ta aikata , tace ta lura cewa an yi amfani da wannan sansanin wajen kai hari kan makaranta a kudancin iran a watan fabareru
Kasar Amurka ta kai hare-hare da dama na keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta akan iran tun daga ranar 7 ga watan Aprilu lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta a yakin da ake yi tsakanin Iran da Amurka da HKI