Kwamandan dakarun kai daukin gaggawa ya yi da’awar kafa gwamnatin hadin kan kasa a birnin Khartoum
Al-Pasha Tabik, mai ba da shawara ga kwamandan rundunar Rapid Support Forces ta dakarun kai daukin gaggawa ya bayar da rahoton cewa, an sanar da batun kafa gwamnatin hadin kan kasa a babban birnin kasar Sudan, Khartoum.
A cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na “X” Tabik ya bayyana cewa: Idan rundunar sojin Sudan ta ki amincewa da zaman tattaunawa kuma ta fi fifita batun neman nuna karfi da ci gaba da rikici, to hakan zai Sanya su sanar da kafa gwamnatin hadin kan kasa a birnin Khartoum
Mai ba da shawara ga kwamandan dakarun kai daukin gaggawan, ya kuma fayyace cewa: Rashin amincewar shugabannin sojojin Sudan da kuma kin shiga zaman shawarwari da kuma fifita zabin ta’azzarar al’amura da yaki, na iya sa a sanar da kafa gwamnati a birnin Khartoum domin kare fararen hula da kuma kwace duk wanihalarci daga shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a kasar Janar Abdul-Fattah Al-Burhan.