Search
Close this search box.

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam Sun Halaka Tare Da Jikkata Sojojin Yahudawan Sahayoniyya

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun kashe tare da raunata sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya a lokacin da suke kutsa kai cikin kudancin Gaza Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun kashe tare da raunata sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya a lokacin da suke kutsa kai cikin kudancin Gaza

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas sun sanar da cewa sun yi sanadin mutuwa da jikkatar sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya a yayin da suke kokarin kutsawa cikin yankin Al-Zaytoun da ke kudancin birnin Gaza.

Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa: Dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun yi wani kazamin artabu da sojojin yahudawan sahayoniyya da suka kutsa kai cikin yankin kudancin Al- Zaytoun a birnin Gaz, inda rahotonni suka tabbatar da cewa an samu mace-mace da jikkata a tsakanin sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya kuma an ga yadda jirgin saman yakinsu mai saukan ungulu ya kawo dauki domin kwashe su.

Tun a safiyar Juma’a ne kafafen yada labaran yahudawan sahayoniyya suka watsa rahoton cewa: Wani lamari mai wahala da tsaro ya faru ga sojojin yahudawan sahayoniyya a kudancin birnin Gaza, yayin da mazauna yankin suka tabbatar da jin tashe-tashen bama-bamai da harbe-harben bindigogi, kafin daga bisani su sake ganin jirage masu saukar ungulu suna sauka da shawagi, lamarin da ke nuni da kwashe wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments