Kakakin cibiyar sojojin kasar Iran rundunar Khatamul Ambiya a nan Tehran ya ja kunnen Amurka dangane da amfani da dukiya ko kudaden kasar da ta tsare a kasashen wajen don bawa wasu kasashen ko kafanoni kamar yanda shugaban kasar Amurka ya fada.
Kamfanin dillancin labaran SINA na kasar Iran ya nakalto Ibrahim Zolfikar na fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa duk wata kasa ko kamfanin da ta karbi kudaden fansa daga hannun Amurka da sunan kudaden asarar da aka yiwa jirgin ruwansa a mashigar ruwa ta Hurmus to su san cewa ba zasu sake wucewa ta mashigar ba.
Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trumop ya bayyana cewa zai yi amfani da kudade da kuma kadarorin kasar Iran da ta tsare a kasashen waje don biyan kamfanoni ko kasashen da Iran ta lalata masu jiragen su a mashigar ruwa ta Hurmuz.
Ibrahim ya kara da cewa “Banda gargadin da mukewa shugaban yan ta’adda Donal Trump na Amurka, mun kara nanata ga kasashe ko kamfanonin da abin ya shafa idan wani ya kuskura ya karbi kudaden fansa daga hannun Amurka da sunan jirginsa da aka lalata a mashigar ruwa ta Hurmuz ta su san cewa ba zasu sake wucewa da mashigar ba”.
Zolfigar y ace, wadan nan jirage sun yi asara ne sabod kin amfani da hanyar da aka ayyana masu ta wucewa daga mashigar ne, bayan sun yaudaru da sojojin kasar Amurka wadanda suka jawo yaki a yankin.