Rahotanni da kamfanin dillancin labarai na meher ya nakalto ya nuna cewa cibiyar sojojin Amurka Centcom ta bayyana ce dakarun su sun kawo karshen hare-haren da suka kai a kasar iran da misalin karfe 10 na dare agogon Amurka a jiya laraba, kuma sun ce sun kawo karshen mummunan harin da suka kai kan kasar iran cikin nasara
cibiyar sojin Amurka ta yi Ikirarin cewa a wannan harin sun samu gwamman wurare dake da alaka da dakarun kare juyin musulunci na iran da suka hada da cibiyar kwamandojin sojoji da wuraren adana makami mai linzami da kuma jiragen sama marasa matuki da cibiyoyin sa ido a bakin teku da kuma dakarun sojin ruwan iran
haka zali acikin wannan bayani sun yi da’awar cewa babban manufarsu ta kai harin shi ne rage iran da kuma dakarun dake neman zama barazana ga sojojin Amurka da jiragen ruwan kasuwanci da kuma kasashen dake makwabtaka da gefe tekun farisa.
Centcom ta yi ikirarin cewa dakarun kare juyin musulunci na iran a ranar 28 ga watan yuli sun kadddamar da wani hari na ba zata da makamai mai linzami na ballistic a kan sansanin sojojin Amurka dake gabas ta tsakiya sai dai an harbo makaman da kuma lalatasu
kwamandan dakarun sojin Amurka daga karshe ya bayyana cewa sama da dakarun sojin Amurka guda dubu 50 ne da har yanzu suke gabas ta tsakiya kuma suna cikin shirin ko ta kwana.