Babban Hafsan Sojin Uganda Ya Gargadi Jakadan Amurka Da Ke Kampala

An baiwa jakadan Amurka William Popp wa’adin ko dai ya nemi afuwar shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ko kuma ya bar kasar Uganda, in ji

An baiwa jakadan Amurka William Popp wa’adin ko dai ya nemi afuwar shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ko kuma ya bar kasar Uganda, in ji babban hafsan hafsoshin tsaron kasar Janar Muhoozi Kainerugaba .

A cikin jerin rubuce-rubucen da aka buga a kan X, Kainerugaba ya ce Popp yana rashin mutunta shugaba Musenevi, tare da tozarta kundin tsarin mulkin Uganda.

“Idan har wannan jakadan na Amurka na yanzu bai nemi afuwar (shugaban kasa Museveni) da kan sa ba kan halinsa na rashin kiyaye kaidoji na diplomasiyya a kasarmu, za mu bukaci ya bar Uganda,” in ji shi.

Ya kuma kara da cewa Uganda na mutunta Amurka , amma tana kara shakku kan aniyarta kan yin aiki da gwamnatin National Resistance Movement, da shugaba Museveni ya kafa, wacce ke mulkin Uganda tun shekara ta 1986.

Tun lokacin da Popp ya zama jakadan  Washington a watan Satumba na 2023, an sanya karin jami’an Uganda cikin takunkumi. A cikin wannan makon kadai, an saka jami’an ‘yan sanda hudu cikin jerin sunayen ma’aikatar harkokin wajen Amurka, bisa zargin cin zarafin bil’adama da suka hada da azabtarwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments