Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa babu batun tattaunawa kan shirin kasar na tace sinadarin Uranium wanda ke a matsayin wani bangare na shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya.
Abbas Araghchi ya kuma ce tattaunawar Tehran da Washington ba za ta haifar da wani sakamako ba idan ana amfani da matsin mata lamba da rashin mutunta juna.
Mista Araghchi ya bayyana hakan ne a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin Iran na mako-mako a birnin Tehran babban birnin kasar, bayan da manzon musamman na Amurka Steve Witkoff ya ce Tehran “dole ne ta kawar da” shirinta na inganta makamashin nukiliya domin cimma matsaya da Washington.
Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da bangarorin ke shirin ganawa a ranar Asabar.
Da ya tabo yunkurin da Amurka ke yi na matsin lamba kan Iran a yayin shawarwarin, ministan harkokin wajen na Iran ya ce: Matsayinmu da ayyukanmu a bayyane suke, ba za su cimma komai ta hanyar matsin lamba ba, idan aka yi shawarwarin a cikin yanayi na mutuntawa, za a iya samun ci gaba, amma babu abin da za a samu ta hanyar matsin lamba ba.
Araghchi ya kuma soki “wasu batutuwa masu cin karo da juna” da ke fitowa daga gwamnatin Trump gabanin tattaunawar ta ranar Asabar.
Dama tun farko Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatullah Khamenei ya bayyana a ranar Talata cewa tattaunawar Iran da Amurka a birnin Muscat na kasar Omani ta yi kyau a matakin farko, sai dai ya kara da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da matukar shakku ga daya bangaren.