Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya godewa mutanen kasar Iraki da gwamnatin kasar kan gagarumin tarba da kuma jana’izar da suka yiwa jagora Shahid Imam Aliyul Khaminaei, a biranen Najaf da Karbala.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka bayan an kammala rakiyar gawaki masu tsarki na Imam Khaminaei da iyalan gidansa a birnan Najaf da karbala na kasar ta Iraki a ranar Laraba.
Ministan ya godewa Jami’an tsaro na kasar Iraki wadanda suka hada da Hashdu Shaabi, Sojoji da yansanda, da kungiyoyi masu sa kai da malamai da daliban addini da kuma shuwagabannin bakilun larabawa daban daban a duk fadin kasar. Wadanda suka taimaka don ganin jana’izar ta gudana a cikin nasara.
Ya ce: Jana’izar Imam Shahid da iyalan gidansa, a kasar Iraki ya kara dankon zumunci da na addini tsakanin kasashen biyu.
Wannan dai shi rakiyar Jana’iza mafi girma a Najaf da kuma Karbala mafi girma a tarihin kasar Iraki na wannan zamanin. Kuma taro mafi girma in banda tarukan 40 na Imam Hussain (a) da ake gudanarwa a cikin watan safar na ko wace shekara.