Masana harkokin tattalin arziki a Kamaru sun bayyana cewa yanzu haka akwai CFA triliyan 5 maƙare a lalitar gwamnatin kasar, saboda rashin kammala ayyukan da suka kamata a yi amfani da su.
Ƙasar ta Kamaru ta ciyo bashin kuɗaɗen ne domin gudanar da wasu muhimman ayyuka da za su amfanar da al’umar ƙasar, amma aka yi wasti da su tamkar ba a ma san da zamansu ba.
masana tattalin arzikin ƙasar sun bayyana cewa wannan shi ne abin da ake kira ƙumbiya-ƙumbiya a harkar kuɗaɗe, a yayin da Hukumar Kula da Lamuran Kuɗi ta Ƙasar Kamaru ta kiyasta cewa waɗannan kuɗade wato CFA tiriliyan 5, kwatankwacin dala biliyan 9 sun isa a gudanar da muhimman ayyuka a rubu’in farko na wannan shekara da muke ciki.
Yayin da wani fitaccen Malami a ƙasar Serge Gordon ke cewa gwamanatin ƙasar ta ce ta kammala shirinta da kasa da kashi 20 cikin 100 na matakin kammala ayyukan da ke cikin kasafin kudin da ta yi, wanda ta tabbatar da cewar abinda ta ware ya yi matukar karanci.
Sannan ma’aikatar kuɗin ƙasar ta bayyana cewa gwamnatin na sane da wannan matsalar, wadda ta bayyana cewa an tsara matakan sake duba dukkanin ayyukan da gano irin matsalolin da kan iya bijirowa, sannan in ya kasance akwai bukata a sake tsara su, kana sauya tsarukan rarraba kudade, ko ma a in da hali a soke shirin fitar kudin gaba daya.