An Gudanar da Zaben Kananan Hukumomi A kasar Afirka Ta Kudu

A jiya Laraba ce aka gudanar da zaben kananan hukumomi a kasar Afrika ta kudu, inda jam’iyyun siyasar kasar suke kokarin samun iko da manya

A jiya Laraba ce aka gudanar da zaben kananan hukumomi a kasar Afrika ta kudu, inda jam’iyyun siyasar kasar suke kokarin samun iko da manya manyan biranen kasar.

Shafin yanar gizo na Afrika News ya bayyana cewa ana gudanar da zaben ne a dai dai lokacinda mafi yawan kasar take fama da karancin ruwan sha na famfo, rashin gine –gine masu inganci, rashin adalci cikin rabon dukiya, da kuma rashin ayyukan yi wanda ya kai kasha 30%, da kuma rashin amincewar mutane da ayyukan gwamnatin kasar.

Labarin ya kara da cewa an bude rumfunan zabe da misalign karfe 7 na safe sannan aka rufe su da misalign karfe 9 na dare.

Mutane kimani miliyon 29 suke da damar kada kuri’unsu, amma a zaben shekara ta 2021 kashi 46% ne kawai suka bayyana a rumfunan zabe.

An tsara cewa mutane miliyon 2.6 ne zasu kada kuri’unsu a cikinkwanaki biyu, amma a jiya mutane miliyon 1.4 ne suka yi hakan.Jam’iyyar ‘The African National Congress (ANC), ne ake zaton zata lashe zaben saboda tana cin moriyar kasancewarta jam’iyyar da ta kubutar da kasar daga mulkin wariyar launin fata

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted