Iran: Shirin Trump Na Lalata Tattalin Arzikin Kasar Iran Ya Lalace

Gwamnan babban bankin JMI Abdunnasir Himmati ya bayyana cewa shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na lalata tattalin arzikin JMI, ya lalace ba tare da

Gwamnan babban bankin JMI Abdunnasir Himmati ya bayyana cewa shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na lalata tattalin arzikin JMI, ya lalace ba tare da ya cimma manufarsa ta karya tattalin arzikin kasar da kuma daga karshe mika kai ga bukatun kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran mehrnews na kasar Iran ya nakalti Dr Himmati yana fadar haka bayan da sakamakon zaben tsakiyar wa’adi na Amurka ya nuna cewa an maida jam’iyyar Trump saniyar ware a majalisun dakokin kasar guda biyu, wato Sanet da kuma Representative.

Kafin haka dai sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent, a ranar 27 ga watan October  ya bayyana cewa zai karya tattalin arzikin JMI a cikin makonni biyu, inda zai takura mata sai an saye dalar Amurka guda kan tuman miliyon 300. Ya ce zasu takurawa JMI sai ta kasa sayar da gangan 100,000 na man fetur a kasuwannin duniya.

Dr Himmati ya kara da cewa, amma gashi mai makon faduwar gwamnatin JMI jam’iyyar Trump ce ta fadi a zaben rabin wa’adi, inda Democrate suka kwace iko da majalisun dokokin kasar guda biyu. Amma babu alamun tattalin arzikin JMI yana kan karyewa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted