Habasha ta umurci wasu jami’an diflomasiyyar Sudan 6 da su fice mata daga ƙasa, kamar yadda wani babban jami’in ƙasar na yankin ƙuryar Gabashin Afirka ya bayyana, lamarin da ke nuni da cigaba da taɓarbarewar dangantaka tsakanin ɓangarorin biyu, akan abin da ya shafi zargin mara wa abokan gaban juna bayan.
Sudan ta zargi Habasha da goya wa dakarun RSF da ke yaƙi da rundunar sojinta baya, a yayin da Habasha ke zargin Sudan din da bai wa ƴan tawayen Tigray da ke arewacin ƙasarta goyon baya.
Zarge-zargen da Sudan da Habasha ke yi wa juna, waɗasnda dukkanin ɓangarorin suka musanta, sun ta’azzara fargabar cewa yaƙi na iya ɓarkewa a tsakaninsu, lamarin da zai faɗaɗa yaƙi a wannan yanki na ƙuryar Gabashin nahiyar Afirka. A ranar Lahadi da ta gabata ce gwamnatin Sudan ta ce ta shigar da ƙorafi a gaban Majalisar Ɗinkin Duniya akan Habasha, tana mai zargin ta da bai wa dakarun RSF damar amfani da yankinta wajen ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa masu ƙunar baƙin wake akan ababen more rayuwa na faraen hula.