Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Saƙon Iran ga jami’an Amurka shi ne cewa; Ba ku da wani zaɓi illa ku fahimci gaskiyar cewa ba za ku iya cin nasara kan Iran ba
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Isma’il Baqa’i, ya yi wa gwamnatin Amurka jawabi, yana cewa: “Ba ku fahimci Iran daidai ba, kuma ba ku fahimci ainihin yanayin juriya, ƙuduri da kuma girman al’ummar Iran ba.”
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Baqa’i ya rubuta a wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, yana mai jawabi ga gwamnatin Amurka: “Tabbas girman kai da jiji-da kai su ne farkon faduwar mutum a fagen rayuwa.”
Ya kara da cewa, “Kwadayinku – wanda ya bayyana a cikin kawancen ku da wata gwamnati ‘yar yaudara – shi ne abin da ya janwo kasarku cikin wani hari na haramtacciyar hanya da laifi a kan Iran. Lissafinku ya gaza, zato naku ya ruguje, kuma an fallasa kurakuran dabarunku daya bayan daya; duk saboda ba ku fahimci Iran da gaske ba, kuma ba ku fahimci ainihin juriya, ƙuduri da kuma girman al’ummar Iran ba.”
Ya ci gaba da cewa: “Mutanen Amurka yanzu sun aika muku da sako bayyananne. Duk da haka, idan kuka ci gaba da yin watsi da gaskiya, ku ka kau da kai ga darussan tarihi, ku ka kuma ci gaba da bin wannan hanya mai hatsari, sakamakon wannan babban kuskure zai fi duk abin da kuka gani a yanzu.”