Iran Tayi Tir Da Kalamai Mai Harshen Damo Da IAEA Ke Yi Kanta

wakilin iran a hukumar nukiliya ta duniya yayi tir da kalamai masu harshen damo da hukumar iaea ke yi kan yuranayom dinta

Babban jami’in doiplomasiya kasar iran a birnin Viyanna ya kalubalanci hukumar kula da makamin nukiliya na duniya  game da kalaman da yayi da ya kira bayyana damuwa game da tarin sinadarin uraniyon na kasar,  da kuma tambayar dalilan da suka sanya bai bayyana irin wanann damuwar game da hare-hare da aka kai kan cibiyoyin nukiliyar iran ba

a cikin wani bayani da ya fitar a jiya laraba babban jami’in na iran yayi tire da kalamai masu harshen  damo da babban darakatan hukumar  ta IAEA Rafael Grossi  yayi , inda ya nuna damuwa game da batun tataccen uraniyom din kasar iran adaidai lokacin da yayi gum da baki kan hare hare da Amurka da isra’ila suka kai kan cibiyoyin nukiliyarta

wakilin na iran ya jaddada cewa cibiyoyin  nukiliyar iran suka karkashin kulawar  hukumar nukiya ta duniya Grosi ya san cewa duk wani gram na abubuwan da ya shafi kayayyakin nukiliyar iran a lissafe yake kuma yana karkashin kulawarta

jami’an kasar iran sun soki Grossi da hukumar IAEA saboda bayyana muhimman bayanai da tayi ga gwamnatin isra’ila ciki har da bayanan da suka gano masana ilimin kimiyar nukiliya na iran wanda daga baya aka kai musu hari kuma aka kashe su

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted