Jagora Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Kowace rana da kowace sa’a ta zame ranar gwagwarmaya da kuma jaddada adawa da babban Shaidan
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Labarin kiyayyar da Amurka ta daɗe tana nuna wa al’ummar Musulmi ta Iran da kuma juriyar dukkan ‘yan Iran masu kishin ƙasa, yanzu ya kai matsayin da kowace rana da kowace sa’a sun zame ranar gwagwarmaya da kuma fuskantar babban Shaidan.
A cikin wani sako da ya fitar a ranar yaƙi da girman kai ta duniya, wanda kamfanin dillancin labaran Mehr ya ruwaito, Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Mujtaba Khemene’i ya jaddada cewa: Wannan rana ta zama alamar “daukakar gaskiya a kan ɓangaren karya,” tare da jaddada cewa nauyin da ke kan al’ummar Iran dangane da Amurka mai laifi ya kara bayyana a fili karara.
Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene’i, yayin bitar shekaru da dama na ƙiyayyar Amurka ga al’ummar Iran a matakai daban-daban, – lokacin da gwagwarmaya take fuskantar “Babban Shaidan” hakan ya zama wani abu da ya dore kuma ya zama gaskiyar da ake rayuwa da ita a kullum – ya jaddada cewa: A kowane mataki, makiya sun ci karo da wata katanga mai karfi da ba ta rushewa, wato hakikanin yanayin da ake ciki a kasa, tare da kudurin al’ummar Iran masu girman daukaka wanda babu abin da zai iya girgiza su.