rahotanni sun bayyana cewa akalla mutum guda daya ya mutu yayin da wasu kuma suka jikkata bayan harin da sojojin isra’ila suka kai da jirgin sama mara matuki kan wani mai babur a kudancin labanon a ciki gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da gwamantin tel aviv ke yi da aka cimma tun watan yuni.
an kai harin ne a yamamcin jiya laraba a garin qabrikha dake yankin Marji’yun kamar yadda kafanin dillancin labarai na kasar labanon ya bayyana, haka kuma sojojin isra’ila sun kai hari a garin mansouri damajdal zoun dake tyre, kuma sun bude wuta a tsibirin Hujeir da Saluki dake tsakanin Marj’iyun da Bint Jubalai da kuma nabatiya
haka zali sojojin na isra’ila sun kunna wuta a wasu gidajen a garin hadatha dake bint Jubali, sai dai babu cikakkun bayani game da adadin gidjen da suka kona kp kuma girmar barnar da suka yi a kudancin kasar ta labanon,
tun ranar 2 a watan maris sojojin Isra’ila sun kaddamar da hari a labanon da yayi sanadiyar mutuwar mutane 4400 tare da jikkata akalla 12400 kamar yadda hukumomin kasar suka fitar da bayanin adadin wadanda a bin ya shafi zuwa yanzu.