kakakin ma’aikatar lafiya ta kasar yamen dake da mazauni a birnin sana’a ta fitar da sanarwar a safiyar yau alhamis cewa daga lokacin da kasar saudiya ta fara kaddamar da yaki kan kasar yamen akalla mutane 266 ne aka tabbatar da sun yi shahada 86 daga cikinsu yara kanana ne, guda 38 uma daga cikinsu mata ne yayin da 641 kuma suka jikkata
kasar saudiya bayan ta kai harin soji kan kasar yamen a shekarata 2015 sai ta killace kasar ,ta sama da kasa da ruwa da hakan ya kara jefa alummar kasar cikin matsanancin talauci, sai kuma Amurka ita ma ta killaceta a shekara ta 2026 daga baya kuma tayi ikirarin cewa ta janye daga wannan mataki da ta dauka
tun tuni gwamnatin kasar yamen tasna aniyar karyar killacewa da aka yi mata inda kasar saudiya ta kaddamar da hari a filin saukar jiragen sama na birnin sana’a inda yaci karo da mayar da martani dakarun kasar, kuma suka samu nasarar koran dakarun dake samun goyon bayan kasar saudiya, suka samu gagarumar nasara kuma suka kwace ikon kula da garin Makha dake gabar teku,
ci gaba da ikon kula da tsibirin rohbardi wato babul mundab yana matsayin wani muhimmin mataki da sojojin suka taka, haka zalika kuma sojojin kasar Yamen sun yi nasarar kwace wasu tsibirai daga hannun sojojin haya dake samun goyon bayan kasar saudiya,