Jami’an diblomasiyya daga kasashen duniya da dama, da kuma wakilan kungiyoyin agaji daban-daban sun hadu a birnin London na kasar Burtania don tattauna batun yakin da ke faruwa a kasar Sudan wanda a halin yanzu yake cika shekaru 2 ke nan.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika New” ya bayyana cewa, taron na kwana guda ya tattara wakilai daga kasashen Faransa, Burtaniya, Jamus da kuma kungiyar tarayyar Turai, har’ila yau da kasashen da suke makobtaka da kasar ta Sudan.
Labarin ya kara da cewa, yakin na Sudan wanda yake cika shekaru biyu, ya zuwa yanzu ya lakume rayukan mutane akalla 20,000, sannan ya yi sanadiyar kauracewar mutane kimani miliyon 14 zuwa cikin kasar da kuma kasashe makobta, sannan wasu da dama ji raunuka.
Ministan harkokin wajen kasar Burtania David Lammy, a jawabin da ya gabatar a taron na ranar Talaya ya bayyana cewa za’a dauki lokaci kafin a dawo da zaman lafiya a kasar ta sudan, Amma abunda wannan taron yake nema shi ne samun wata kafa ta isar da kayakan agaji ga wadanda suke tsananin bukatarsu a yankuna daban daban na kasar da kasashe makobta.