Gwamnatin Amurka ta amince da shirin mikawa HKI dubban boma-bomai saboda kashe falasdinawa a Gaza.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, sojojin HKI suna jiran isowar boma-bomai daga kasar Amurka don fara wani aikin soje na musamman a Gaza. Saboda kawo karshen samuwar Falasdinawa a yankin.
Wata majiyar HKI, yahudawa ta fadawa kamfanin dillancin labaran ‘Ynetnews’ kan cewa sojojin sama na HKI su na dakon isowar boma-bomai har 3000 daga kasar Amurka a cikin yan makonni masu zuwa.
Labarin ya kara da cewa rundunar ta na son ta gudanar da ayyukan soje mai fadin gaske a kan Falasdinwa wanda ya zai kawo karshen Hamas ya kuma kawo karshen samuwar Falasdinawa a yankin.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin kasar Amurka ta na shirin aiko da wani karin boma –bomai har 10,000 nan gaba. Yahuda zasu yi amfani da wadannan boma-boman don fadada ayyukansu a yankin, wadanda suka hada da Siriya da Lebanon da kuma ita Gaza.