Rundinar Amurka ta CENTCOM ta ce sojojin Amurka sun sake toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran da hana jiragen ruwanta zurga zurga, duk da gargadin da Jamhuriyar Musulunci ta yi cewa Washington ba za ta iya sake bude mashigin Hormuz da karfi ba, wanda Tehran ta rufe saboda keta dokokin Amurka.
CENTCOM ta ce a halin yanzu akwai jiragen ruwan yaki sama da 20 na Amurka da daruruwan jiragen sama na soja da ke cikin shiri” a fadin yankin.
A kwanan baya ne shugaban Amurka Donald Trump, ya shure yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu suka sanyawa hannu a shiga tsakanin Islamabad.
A karkashin yarjejeniyar, Iran ta amince ta ba da izinin zirga-zirgar jiragen ruwa kyauta ta cikin mashigar ruwa na tsawon kwanaki 60.
A bisa ga yarjejeniyar, Jamhuriyar Musulunci ta tsara wata hanya ta musamman ta ruwa ga jiragen ruwa don wucewa a mashigar, tana gargadin jiragen ruwa kan amfani da hanyoyin da ba bisa ka’ida ba.
Duk da haka, Amurka ta yi kokarin raka jiragen ruwa ta mashigar ta wata hanya, wanda hakan ya sa Jamhuriyar Musulunci ta rufe hanyar har sai Washington ta kawo karshen katsalandan da take yi wa harkokin sifirin jiragen ruwa a yankin.
Kafin sanarwar, CENTCOM ta tabbatar da “kai hare hare bisa abinda ta bayyana da cewa murkushe tasirin Iran wajen kai hare-hare kan jiragen ruwa a mashigar.