Al’ummar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yakin da ake yi a Gaza
A karkashin taken “An rusa Gaza” kuma goyon bayan al’umma ga Falasdinawa abu ne da ya zama wajibi, ba zabi ba, mazauna birnin Nouakchott fadar mulkin kasar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zanga domin jaddada bukatar musulmi a ko’ina a duniya su goyi bayan gwagwarmayar da ake yi a Zirin Gaza.
Zanga-zangar dai ta samu halartar kungiyoyin ‘yan jaridu da sauran kungiyoyi da dama, wadanda suka bayyana Allah wadai da shirun da manyan kasashen duniya suka yi, tare da sukar su kan goyon bayan sojojin mamayar Isra’ila.
Wani sheikhin malami dan kasar Mauritaniya ya ce: “Sun sanar da mu irin wannan gagarumin aiki, Allah Ya saka musu da alheri kan irin wannan zanga-zangar da suke yi na goyon bayan wadanda ake zalunta ta hanyar kashe mata da yara da kuma tsofaffi da suke yunkurin kare hakkokinsu.
Masu zanga-zangar sun yi kira da a yanke alaka tsakanin kasarsu da Amurka da duk masu goyon bayan yahudawan sahayoniyya a yakin da suke yi na neman shafe Falasdinawa daga kan doron kasa tare da azabtar da su da masifar yunwa a zirin Gaza.