Al-Adu Da Cikin Addinin Musulunci A Tarihi 10

10-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-adu da ci gaban addini addinin musulunci a tarihi, wanda

10-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-adu da ci gaban addini addinin musulunci a tarihi, wanda ni tahir amin yake kawo mako sau guda a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun tsaya inda muka yi magana dangane da gano takarda da kuma tasirinsa a ci gaba da kuma wayewar musulmi, a farko farkon bayyanar sa. Mun bayyana cewa gano takarda ko kuma littafi ya sawwaka karatu, da kuma tarjama. Tare da tarjama wasu sabbin ilmi sun shiga cikin al-ummar musulmi, suka kuma haddasa sauyi masu yawa a cikinsu, wasu na da kyau, wasu kuma sun rikita akidun addnin musulunci ga wadanda basu fahinci addinin ba, ko basa tare da iyalan gida manzon All..(s).

Amma wadanda suke tare da su, wadanda yan kadan ne sosai, basa rikicewa saboda shigar sabbin akidu cikin musulmi, saboda Limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) suna nan a madakata. Ko kuma a lokacin gaiba, malaman mazhabar suna nan suna warware matsalolin da suka shafi akida.

Sannan mun bayyana cewa hatta bayan rauni da ma faduwar daular musulunci a hannun mungoliyawa, ko kuma a farkon karni na 20 bayan yakin duniya na daya da kuma faduwar daular Uthmania a hannun turawa, musulmi, larabawa da wadanda ba larabawa ba suna rike da al-kur’ani suna karatunsa, ta yanda a wasu lokuta, hatta larabawa ba su fi wadanda ba larabawa iya karatun al-kur’ani, musamman lafuzzansa kamar yanda yake a asali, duk da cewa basa fahintar ma’anar abinda suke fada da larabaci ba, a wasu lokutan.

Babu bambanci, a cikin al-kur’anai wadanda ake bigawa a Masar da Saudia da Lebanon da kuma Iran ko Iraki ba. Ana gudanar da gasar Alkur’ani ta kasa da kasa, a Saudia da Masar da iran da iraki, musulmi shia da  sunnan suna halattar su, amma basu taba cewa a kwai bambanci a tsakanin bugun Masar da na Iran ko saudia da Iran ba.

Tarihin larabawa kafin musulunci ya nuna cewa, akwai wadanda suka iya rubutu da karatu. Sai dai basu da yawa, mafi yawan karatunsi hadda ce, daga baki zuwa baki. Wannan kasidu ne ko kuma maganganu masu hikima, sannan musulunci ya sami wannan zamanin. Don haka duk tare da cewa sabbai da dama sun iya rubutu da karatu, amma mafi yawansu sun dogara da haddar abinda suka ji wajen manzon All .. (s) na Alkur’ani da hadisai. Wannan duk da cewa akwai wadanda suka rubuta su. Suke kuma adanasu don al-umma ta gabata.

Don haka kauyawa da dama suna rare kasidu suna nakaltan kissoshin da suka haddace a cikin larabci amma kuma basu iya karatu da rubutu ba. Don haka wanda ya binciki tarihim larabawa zai ga wasu al-amura da suka nuna cewa wasu sun iya  rubutu da karatu. Akwai rubutu kan duwatsu wadanda mutum yake iya karatu ya fahinci abinda ake nufi da su. Hatta wasu kasidun jahiliya ana da su. Malamai da dama sun tattarasu, cikin littafai wadanda ake kiransu wakokin jahiliya.

A kasar Hijas ana da irin wadan nan rubutun, sannan malaman tarihi sun bayyana cewa, rubutun da yafi yaduwa a lokacin a Hijaza shi ne rubutun NABATIY.

Ibn Nadim daya daga cikin malaman tarihi da kuma bincike dangane da rubutu da littafi, ya kawo a cikin littafinsa da akekira Alfehrest, ana da wani tsohon hannun rubutu wanda ake danganta shi da Abdulmuttalib, kakan manzon All..(s), wanda aka samu a dakunan ajiyar kayakin tarihi na sarki Ma’amun dan Sarki Harunan Rashid daya daga cikin sarakunan Abbasiyawa.

Banda haka wasu ayoyin Alkur’ani mai girma sun nuna cewa, a farkon bayyanar addinin musulunci larabawa sun san rubutu da karatu amma ba kwararru ne a cikinsa ba.

Kalmomin Kitab littafi da Sahifa, shi ma littafi, duk suna nuni kan cewa larabawa sun san menene rubutu ko karatu. Hakama ma a wata ayar an kawo Kalmar Alkalami.

A wasu ayoyin All.. ya bukaci musulmi su rubuta basussuka da ke tsakaninsu, a bawa wanda aka karbi bashi a hannunsa ya rike don ya zama sahida gareshi. A wata Aya a cikin suratul Bakara All.. yana fada a aya ta 282:

{Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi mu’ãmalar bãyar da bãshi zuwa ga wani ajali ambatacce, sai ku rubũta shi. Kuma wani marubuci ya yi rubũtu a tsakaninku da ãdalci. Kuma kada marubũci ya ki rubũtãwa, kamar yadda Allah Ya sanar da shi, sai ya rubũta}.

Bisa umurnin da ya zo cikin wannan ayar, yakamata musulmi su rubuta basussuka dake tsakaninsu, da ajalin da bashin zai kare, wanda ya nuan daga tarihin da aka bayar. Don haka ta umurcesu da su koyi lissafin kwanaki da lokuta a shekara, su ayyuana ranar da bashin zai kare ko a jalinsa, wanda yakamata ya kasance a lokaci na gaba daga kwanaki zuwa watanni ko shekaru.

Har’ila yau ta koya wa musulmi ajiye rubutu da shaidu da kuma duk wani abu mai muhimmanci wand aba kamata a manta da shi ba.

Amma abin mamaki shi ne, khalifofi na farko bayan manzon All..(s) sun haramta a rubuta hadisansa (s) wanda ya jawo batar wasu da dama, sun kona wasu sun lalata wasu, da sunan kada su rikice su hadu da al-kur’ani mai girma. Sai bakin shekaru kimani 100 bayan hajira, bayan da dama daga sahabban manzon All..(s) sun mutu, wasu sun tsufa, sai aka fara rubutun hadisansa(s).

Wannan kuma ya budewa masu karya wa manzon All..(s) suka yi ta yin karya, sannan hadisan Isra’ilawa wadansa suka musulunta, da dama suka shigo cikin wadanda aka tattara daga bayan. Natijarsa shi sabawa ni mai yawa a cikin musulmi, a cikin al-amura da dama, a fassarar alkur’ani ko a fahintar huknce hukuncen shari’a.

Wadanda basu rikice sosai ba, su ne wadanda suke tare da iyalan gidan manzon All…(s), su ma basu tsira kwata kwata ba, amma suna da mafita mai aminci. Wanda ba zaka kwatantasu da sauran mazhabobin musulmi ba.

Dangane da wannan, manzon All..(s) ya ambaci al-amura da dama dangane da rubuyu da ilmi da kuma littafi, kamar inda yake cewa {Ku daure ilmi da rubutu}, wato idan kuna son ilmi ya zauna a cikin kwokwalenku, to ku rubuta shi a takarda, idan ba haka ba, zaku yi ta karatu amma ba zai zauna a kwakwalenku ba, sai kun daure shi da rubuta.

A wani bangare kuma, manzon All..(s) yana da wasu zababbun mutane, wadanda suka rubuta masa, ayoyin alkur’ani da aka saukar masa. Ko kuma wasu littafai da ayyukan gwamnati, daga cikinsu akwai Aliyu dan Abitalib (a).

A lokacin dai samun fata yana da tsada ko yana da wuya, wadanda basa da hali basa  iya amfani da fata a duk lokacinda suke so.

Sai dai an sami wasu rubuce rubucen Abdul muttalib (kakan manzon All..(s) a kan fatar dabbobi. Ana amfani da fata wajen rubuta al-amura masu muhimmanci, saboda yana dadewa bai lalace ba.  An ci gaba da amfani da fata saboda rubutun al-amura masu muhimmanci har zuwa tsakiyar daular Abbasiyawa a lokacinda takardu masu inganci suka shiga kasuwa, kuma kowa yana iya samunsu da sauki.

A lokacin su kan yi amfani da fata ne kawai don rubuta abubuwa masu muhimmanci a wajen gwamnati,  kamar alkawula. Da hukunce hukuncen sharia, da wadanda suka yi kama da su.

An nakalto hadisi daga Ummu Salma ummul muminina matar manzon All..(s), tana cewa wata rana manzon All..(s) ya nemi fata don rubutu aka kawo masa, sai yana fada Aliyu dan Abitalib (a) yana rubutu, har ya cika ta da bayanta da kuma gefenta da rubutu.

Kafin takarda Larabawa su kan yi amfani da katsin dabbobin gida rubutu, musamman kashin rakumi da akuya da bawo ko rassan itaciyar dabinon da suka bushe. Ko yadin Kellen al-hariri fari. Ko kuma fatar da ake jeme, suna amfani da shi a rubuce rube ce a lokacin. Malaman tarihi sun nakalto cewa an sami rubuce rubuce aka aka yi musayarsu, tsakanin daddaikun mutane, da shuwagabanni a rabin farko na karnin hijira.

A lokacin, wasikun da suka fi shahara, su ne wasikun Aliyu dan Abitalib (a) a lokacin Khalifancinsa, wadanda wasunsu sun zo a cikin littafin Nahjul  Balagha.

Banda haka, musulmi sun amfana da irin ci gaban da kasashe makobta suka samu a bangaren rubutu da karatu, don ci gagan ilmi da ilmantarwa a tsakaninsu.  Mun san cewa bayan da musulmi suka sami iko da kasashen Masar da Sham sun fara amfani da takarsa, kuma daga lokacin harkokin rubutu da karatu suka fara sauki.

Don haka tun zamanin Umayyawa da kuma Abbasiyawa, takarda ta fara samuwa a tsakanin musulmi, a kasashen Iraki, Masar da Sham, sai ta zama kowa da kuwa yana iya amfani da ita.

Malaman tarihi sun bayyana cewa a zamanin Khalifa Mansur Dawaniki, daya daga cikin sarakunan Abbasiwa, ya sami cewa an tare takardun rubutu masu yawa a dakin ijiyarsu, sai ya bada umurnin a kaisu kasuwa a saida su ga mutane. Sabode a samar da filin ajiyar kayakin gwamnati sannan a yi amfani da kudaden don kyautata ayyukan gwamnati. Amma daga baya, ya dakatar da sayarwan, saboda tsoron karancin su a fadarsa. 

Daga karshe a rabin karni na farko, zuwa na biyu bayan hijira, takarda da kuma fata suna samuwa a ko ina, daga kasar China, sannan hatta musulmi sun bude masana’antun samar da takardu da fata a cikin kasashen musulmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted