Ahmad Dawud Uglo Ya Sanar Da Ficewa Daga Jam’iyar Mustaqbal Kuma Ya Rusata

Shugaban jam’iyar mustaqbal na kasar turkiya Ahamd Dawud Uglo ya sanar da ficewa daga jam’iyar mustaqbal kuma ya rusata, kuma ya bayyana cewa wannan matakin

Shugaban jam’iyar mustaqbal na kasar turkiya Ahamd Dawud Uglo ya sanar da ficewa daga jam’iyar mustaqbal kuma ya rusata, kuma ya bayyana cewa wannan matakin ba ya nufin mika wuya , wani mataki ne na kyawawan halaye.

haka zalika Uglo yace matakin da ya dauka na rusa jam’iyar mustaqbal ta zo ne bayan kasa hada kan yayan jam’iyar karkashin inuwa daya,yace zargin cin hanci da rashawa da ake yi yayi mummunar illa ga rayuwar siyasa a fadin kasar turkiya

Dawud Uglu ya dauki tsarin siyasa na kasar Turkiya a matsayin wanda ruwa ya kare masa, don haka yayi kira da a yi juyin juya hali na kwakwalwa a wannan bangaren, yace zai ci gaba da gudanar da ayyukan sa a fagagen tunani da koyarwa da wayewa da tattalin arziki da zai taimaka wajen sake gina sabuwar turkiya don gobe mai kyau.

An daukar Ahmad Dawud Uglu a matsayin daya daga cikin fitattun yan siyasa a turkiya inda ya kasance ministan harkokin  wajen kasar a shekara ta 2009 zuwa 2014 , kuma ya zama fira minista daga shekara ta 2014 zuwa 2016 wanda a shekara ta 2019 ya kawo karshen zamansa a jam’iyar Adalci da ci gaba, kuma ya kafa jam’iyar mustaqbal da ake dauka a matsayin daya daga cikin fitattun jam’iyu  masu karfi dake zama kalubale ga jam’iyya mai mulki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted