Afirka Ta Kudu Da Rwanda Basa Cikin Shirin Kasuwanci Na Amurka-Afirka

Gwamnatin kasar Amurka ta fidda kasashen Rwanda da Afrika ta kudu daga shirin kasuwanci na Afrika da Afirka, inda sauran kasashen zasu sami damar shigo

Gwamnatin kasar Amurka ta fidda kasashen Rwanda da Afrika ta kudu daga shirin kasuwanci na Afrika da Afirka, inda sauran kasashen zasu sami damar shigo da ragin da ake samu a kasuwanci da ita.

Shafin yanar gizo na Africanews ya bayyana cewa, Amurka ta dauki matakin kan wadan nan kasashe biyu ne saboda wasu matsaloli da suka shafesu.

Kasar Ruwanda dai, saboda hannun da take da shi a goyon bayan da take bawa kungiyar yan ta’adda M23 a kasar Democradiyyar Kwango, inda a cikin yan watannin da suka gabata ma, sai da Amurkan ta dorawa ministan harkokin wajen kasar takunkuman tattalin arziki.

Gwamnatin kasar Rwanda dai ta musanta wannan zargin ta kuma bayyana cewa rikicin kasar Kwanco ta cikin gida ne kuma bata da hannu a cikinsa.

Amma kasar Afirka ta kudu kuma gwamnatin Amurka tana zarginta da abinda ta kira nuna bambancin launin fatan da take nuna yan kabilar Afrikana. Wato tsirarun fararen fatan kasar. Wanda ita ma Afrika ta kudu ta musanta hakan, sannan ta bayyana cewa wareta daga wannan shirin zai cutar da kasashen biyu.

Shirin harkokin kasuwanci na Amurka-Afrika dai ana sabonta shi a ko wace shekara, kuma a wannan karon zai fara daga watan Jenerun shekara ta 2027-2028.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted