Kakakin sojojin Kasar Yemen ya bada sanarwan cewa a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata, mutane akalla 8 ne suka rasa rayukansu, sanadiyyar hare hare kan wurare daban daban a kudancin kasar Yemen.
Kamfanin dillancin labaran Mehrnews na kasar Iran ya bayyana cewa, Burgediya Yahyah Saree ya bayyana haka ne a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, jiragen yakin saudiya sun kai hare hare har guda 109 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata a kan Lardunan Sa’aad, Ta’izz, Lahij Al-Jauf da kuma Hudaydah.
Saree ya kara da cewa, wannan ya kawo adadin mutanen da kasar saudia ta kashe tun bayan fara yakin a cikin watan Yulin da ya gabata zuwa 3,939. Ya kara da cewa gwamnatin Saudia tana amfani da jiragen yaki samfurin F-15SA da kuma Eurofighter Typhoon wadanda suke tashi daga sansanonin sojojinsu na Sarki Khalid kusa da garin Khamis Mushait da kuma na sarki Fahd da ke garin Taif don aiwatar da wadan nan hare hare.